Tsaro

Ƙungiyar Dattijan Arewa(ACF) ta tona asirin wata sabuwar hanyar shigo da makamai Arewa.

Spread the love

Bisa wani dogon binciken sirri da kungiyar dattijan Arewa ta ta yi don taya shugaba Buhari dakile ta’addanci a Najeriya, kungiyar ta tona asirin wata sabuwar hanya da ake shigo da makamai Arewa.

Kungiyar ta bayyana cewa an koma amfani da rakuma wajen safarar manyan bindigu na harbo jirgin sama ta kan iyakokin da ke Arewa, musamman jihohin sokoto da zamfara.

Haka kuma kungiyar ta bayyana yadda ‘yan ta’adda ke samun kudin sayen makamai daga kasashen ketare.

Kungiyar ta ce ‘yan bindiga na samun kudin sayen makamai ne daga kudin fansa da suke tatsa daga hannun jama’a.

Shugaban kungiyar Chief Audu ogbeh ya kara da cewa ana shigo da makaman ne daga makwabtan kasashen da ke makwabtaka da Najeriya, amma bai ambaci sunayen kasashen ba.

Chief Audu Ogbeh ya ce mambobin kungiyar ta su ne suka sanar da su haka, kuma kungiyar ta ce hakki ne akan su su sanar da gwamnatin tarayya wannan makircin domin daukar matakin gaggawa.

Daga Kabiru Ado Muhd.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button