Ƙungiyar Marubutan Arewa A Kafofin Sadarwar Zamani “Arewa Media Writers” Ta Ƙaddamar Da Shugabannin Ƙungiyar Reshen Jihar Sokoto, Tare Da Basu Takardun Shaidar Kama Aiki Nan Take
….Haza zalika ƙungiyar ta karrama wasu daga cikin manyan jihar da suke yi wa al’ummar jihar Sokoto hidima ba dare babu rana.
Daga: Ƙungiyar “Arewa Media Writers”
Ƙungiyar Marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani ta ƙasa wato “Arewa Media Writers” ta ƙaddamar da shugabannin ƙungiyar reshen jihar Sokoto, tare da basu takaddun kama aiki nan take.
Ƙaddamar da shugabannin ƙungiyar reshen jihar Sokoto, ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, da sauran shugabannin ƙungiyar na kasa, taron ya gudana ne a sabon babban ɗakin taro na “NEW ICT CENTER SSCOE” dake cikin kwaryar Jihar Sokoto.
Taron ya samu halartar manya manyan baƙi da Sarakuna daga sassan jihar, da suka hada da mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Sokoto, a ɓangaren harkokin matasa Nuradeen Harande Mahe, da kuma uban ƙungiyar reshen jihar Sokoto, kuma mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Alhaji Yusuf Dingyadi, da mai kula da harkokin aikace aikacen Gwamnan Jihar Zamfara (PPS) Dakta Lawan Maradun, da sarkin yakin Gaji Alh. Sani Jabbi, da shugaban kungiyar matasan jihar Sokoto Amb. Yakubu Abubakar, da shugaban kungiyar “Sokoto Reload” Nuradeen Muhammad Mahe, da Hajiya Fatima Mai Gari, da Alhaji Kabiru Aliyu Foundation, da Engr. Mustapha Muhammad da Abdullahi Shehu Foundation da sauran shugabannin da suka fito daga sassan jihar da membobin ƙungiyar.
Ƙungiyar ta tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi ci gaban yankin mu na Arewa.
Shugabannin ƙungiyar reshen jihar, sun yi farin ciki tare da annashuwa kan yadda aka gabatar da taron ƙungiyar, cikin lumana da ƙarawa juna sani kan ayyukan da suka shafi ƙungiyar, tare da yin alkawarin za su gudanar da ayyukan ƙungiya kamar yadda dokar ƙungiya ta tana da.
Jadawalin Shugabannin Ƙungiyar “Arewa Media Writers” reshen jihar Sokoto, tare da mukamman su
👇👇👇👇
- Bashar Mustapha Bashar, a matsayin Shugaban ƙungiyar reshen jihar Sokoto, wato (Chairman Sokoto State).
- Dr. Abubakar Umar Gidan Madi, a matsayin mataimakin shugaban ƙungiyar reshen jihar Sokoto wato (Deputy Chairman Sokoto State).
- Dr. Abdulganiyyu Abubakar Romo, a matsayin Magatakardar ƙungiyar reshen jihar Sokoto, wato (Secretery General Sokoto State).
- Abdullahi Sani Sokoto, a matsayin mataimakin magatakardar ƙungiyar reshen jihar Sokoto, wato (Assistant Secretary Sokoto State).
- Tahamu Muhammad, a matsayin babban jami’i mai kula da asusun ƙungiya, ma’ajin ƙungiya, reshen jihar Sokoto, wato (Director of Finance Sokoto State).
- Fatima Hamdany,, a matsayin babbar jami’a mai kula da kadarorin ƙungiya, reshen jihar Sokoto, wato (Sales Director Sokoto State).
- Sabitu Umar, a matsayin babban jami’i mai sa’ido da bincike kan ayyukan ƙungiya, reshen jihar Sokoto, wato (Auditor General Sokoto State).
- Bashir Almustapha, a matsayin babban jami’in ƙungiya mai sharhi, fashin baki, reshen jihar Sokoto, wato (Editor Sokoto State).
- Junaidu Yusuf Sokoto, a matsayin babban jami’i mai kula da tsare tsaren ayyukan ƙungiya a lokutan gabatar da taro ko wasu ayyukan ƙungiya, reshen jihar Sokoto, wato (Organizing Secretery Sokoto State).
- Abdulrahman Muhammad Goshe, a matsayin mataimakin babban jami’i mai kula da tsare tsaren ayyukan ƙungiya a lokutan gabatar da taro ko wasu ayyukan ƙungiya, reshen jihar Sokoto, wato (Assistant Organizing Secretery Sokoto State).
- Yusuf Muhammad, a matsayin Babban jami’i mai magana da yawun bakin ƙungiya reshen jihar Sokoto, wato (PRO 1 Sokoto State).
- Comrade Abdullahi Aliyu, a matsayin mataimakin babban jami’i mai magana da yawun bakin ƙungiya reshen jihar Sokoto, wato (PRO 2 Sokoto State).
- Zainul Abideen Sa’id, a matsayin babban Jami’i mai kula da ci da sha na ƙungiya reshen jihar Sokoto, wato (Welfare Director Sokoto State).
- Sufiyanu Abubakar, a matsayin babban jami’i mai ladabtarwa reshen jihar Sokoto, wato (Discipline Sokoto State).
- Shehu Ibrahim Goronyo, a matsayin babban jami’i mai daukan hoto, tace hoto, reshen jihar Sokoto, wato (Design Picture & Photography Sokoto State).
Ƙungiyar “Arewa Media Writers” tana da shugabanci a dukkannin ƙananan hukumomi 23 dake jihar Sokoto, da suka haɗa da:-
1, Chairman
2, Secretary
3, Editor
4, Organizing Secretary
5, PRO.
Ƙungiyar tana da membobi a kowacce ƙaramar hukuma dake faɗin jihar.
Nan bada daɗewa ba uwar ƙungiyar za ta ci gaba da kewa yawa sauran jihohin dake Arewa cin Nijeriya, domin ƙaddamar da shugabannin ƙungiyar reshen sauran Jihohin.
Haza zalika ƙungiyar ta karrama wasu daga cikin manyan jihar da suke yiwa al’ummar jihar Sokoto hidima ba dare babu rana, da suka hada da; Hajiya Fatima Ahmad Maigari da Alhaji Kabiru Aliyu Foundation da Eng Mustapha Muhammad da Abdullahi Shehu Foundation.
Ƙungiyar “Arewa Media Writers” tana kira ga Al’umma da su ba ƙungiyar haɗin kai tare da goyon baya domin kawo wa yankin Arewa da ƙasar Nijeriya bakiɗaya ci gaba.
Ƙungiyar “Arewa Media Writers” tana buƙatar Addu’o’i daga gare ku Allah ya shige mata gaba kan muhimman ayyukan da ta saka a gaba, na ganin ta kawo canji a yankin mu na Arewa.