Kungiyoyi

Ƙungiyar NANS Ta Yi Barazanar Fara Zanga-Zanga Idan Ba A Janye Karin Farashin Mai Ba.

Spread the love

Kungiyar Dalibai ta Kasa a Najeriya (NANS) ta gargadi gwamnati kan karin farashin man feturn, tare da sheda cewa, idan gwamnatin ba ta sauya karin farashin man fetur din ba, to kuwa za ta fuskanci gagarumar zanga-zangar dalibai a fadin kasar.

Bayanin kungiyar ya ce abu ne mai kada rai matuka, ta yadda aka daga farashin mai a rana guda daga N145 zuwa N161.

Mataimakin shugaban kungiyar Dalibai (NANS), Kwamared Ojo Raymond ya fada a cikin wata sanarwa cewa, sabon farashin da aka sanar ya nuna cewa gwamnati ba ta damu da halin da jama’ar kasa suke ciki ba.

Sanarwar ta ce ko shakka babu daliban Najeriya ba su amince da wannan karin farashi ba, domin hakan zai kara dagula rayuwar jama’ar kasa tare da kara jefa su cikin wani halin na tsananin rayuwa da suke ciki.

Haka nan kuma bayanin kungiyar daliban ya yi ishara da cewa, karin farashin man wanda ya zo bayan karin farashin wutar lantarki, wanda dukkanin wadannan matakai ne na kuntata wa jama’ar kasa, musamman marasa karfi daga cikinsu, wadanda su ne suka fi yawa a tsakanin al’ummar kasa.

Sai dai a cikin wani bayanin shugaba Buhari wanda mataimakinsa Yemi Osinbajo ya karanta a yau, ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya kan batun karin farashin man fetur a Najeriya, sai rashin yin hakan zai haifar da wasu matsalolin na daban.

Daga Haidar H Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button