‘Ƴan karota sunyi sanadiyyar mutuwar wani Bawan Allah direban mota A jihar Kano.
Rahotanni da muke samu daga jihar Kano ta Hanyar wani ganau Mai suna Abba Adam Isah Ya Tabbatar da mutuwar wani Bawan Allah Wanda Yace ‘yan karota ne sukayi sanadiyyar mutuwarsa
Malam Abba Ya Rubuta A shafinsa na Facebook Yana Cewa Innailillahi wa’innailaihirrajiun,
Yanzu ina tafiya zani rijiyar zaki daidai BUK Old site ƴan KAROTA suka tare mu wai lokacin sanitation ya shiga mun tsaya muna basu baki amman ba tamu suke ba suka cigaba da saka wasu karafuna suka datse titi can sai ga wani mutumi cikin Mercedes Bai kula dasu ba kuma motarsa bazata riƙu ba haka yaje ya afka cikin kwata sai gawarsa. Nan take da suka ga mutane sun taso musu , sai suka hau motarsu suka gudu.
Allah ya gafarta masa
Amman ƴan KAROTA abunda sukeyi ya wuce Gona da iri wallahi 😢