Labarai

Ɗorawa Shugaba Buhari laifi akan matsalar tsaro da ‘yan Najeriya suke yi babban kuskure, in ji tsohon Shugaban Ƙasa IBB.

Spread the love

Bai kamata mutane su rika ganin laifin Shugaba Buhari kadai akan rashin tsaron da ya addabi Arewa ba, in tsohon Shugaban kasa IBB.

Tsohon Shugaban Najeriya na mulkin Soja Janar Ibrahim Badamasi Banbangida ya ce bai kamata ‘yan Najeriya su rika ganin laifin Shugaban kasa Muhammadu kadai akan matsalar tsaron da ta addabi ƙasarnan musamman yankin Arewa ba.

Janar Babangida ya ce dorawa Shugaban kasar laifi shi kadai da ‘yan Najeriya suke yi babban kuskure ne indai ba zasu rika hadawa da gwamnoni da sarakauna da sauran masu rike da madafun iko ba.

Tsohon Janar din ya kara da cewa Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari shi shi kadai ba zai iya shawo ko magance matsalar tsaron da Najeriya ta tsinci kanta a ciki ba har sai ko wanne bangare na masu rike da madafun iko tun daga kan gwamnoni, sarakuna, da su Kansu ‘yan kasar sun zage dantse wajen taimaka masa ta ko wanne hali bisa doron doka.

Babangida ya ce yana shawartar gwamnonin Najeriya da Sarakuna da duk wani ‘yan kasa da su tashi tsaye su hada kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da nasarar da shi Shugaban kasar ya taso agaba.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana haka ne yayin nuna farin cikin sa da sako Ɗaliban makarantar Sakandiren kagara ta jihar Neja da masu Garkuwa da mutane sukayi yau.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button