Lafiya

Ɗaya daga cikin membobin kungiyar “Arewa Media Writers” ya kaddamar da sabon asibiti a Jihar Taraba, domin ya saukakawa al’ummar Jihar

Spread the love

A yammacin ranar Lahadi 07/03/2021 Shugaban ƙungiyar “Arewa Media Writers” reshen jihar Taraba Malam Osama Bello Isa Jalingo, ya jagoranci tawagar ƙungiyar zuwa bude sabon Clinic mai suna YESMEN CLINIC AND MATERNITY wanda ɗaya daga cikin Hazikan ‘yayan ƙungiyar Alhaji Maiwada Atake Jalingo, ya samar domin sauka kawa Al’ummar jihar.

Surayya Muhammad Maigari ɗaya daga cikin wakilan ƙungiyar “Arewa Media Writers” na ƙasa ita ce ta wakilci tawagar matan social media a wajen taron, Malama ta nuna farin cikinta, da kuma isar da sakon taya murna a madadin ƙungiyar mai Albarka bakiɗaya.

Daga ƙarshe Shugaban ƙungiyar na jaha Malam Osama Bello Isa, ya shaidawa jama’a cewa irin wadannan Ayyuka domin al’umma yana ɗaya daga cikin manyan manufofin wannan ƙungiyar, saboda haka yana kira zuwa ga masu hali na jihar Taraba su yi koyi da hali irin na Alhaji Mai Wada, wajen zakulo matsalolin al’umma da kuma share musu hawaye nan take.

Ya kuma yi Addu’a Allah ya sanya Albarka cikin wannan Clinic ya kuma sakawa Alhaji Mai Wada da mafificin Alkhairi.

Rubutawa✍️✍️
ABUBAKAR NTA,
EDITOR “AREWA MEDIA WRITERS” TARABA STATE.

Ɗaya Daga Cikin Membobin Kungiyar “Arewa Media Writers” Ya Kaddamar Da Sabon Asibiti A Jihar Taraba, Domin Ya Saukakawa Al’ummar Jihar

Daga: “Kungiyar Arewa Media Writers”

A yammacin ranar Lahadi 07/03/2021 Shugaban ƙungiyar “Arewa Media Writers” reshen jihar Taraba Malam Osama Bello Isa Jalingo, ya jagoranci tawagar ƙungiyar zuwa bude sabon Clinic mai suna YESMEN CLINIC AND MATERNITY wanda ɗaya daga cikin Hazikan ‘yayan ƙungiyar Alhaji Maiwada Atake Jalingo, ya samar domin sauka kawa Al’ummar jihar.

Surayya Muhammad Maigari ɗaya daga cikin wakilan ƙungiyar “Arewa Media Writers” na ƙasa ita ce ta wakilci tawagar matan social media a wajen taron, Malama ta nuna farin cikinta, da kuma isar da sakon taya murna a madadin ƙungiyar mai Albarka bakiɗaya.

Daga ƙarshe Shugaban ƙungiyar na jaha Malam Osama Bello Isa, ya shaidawa jama’a cewa irin wadannan Ayyuka domin al’umma yana ɗaya daga cikin manyan manufofin wannan ƙungiyar, saboda haka yana kira zuwa ga masu hali na jihar Taraba su yi koyi da hali irin na Alhaji Mai Wada, wajen zakulo matsalolin al’umma da kuma share musu hawaye nan take.

Ya kuma yi Addu’a Allah ya sanya Albarka cikin wannan Clinic ya kuma sakawa Alhaji Mai Wada da mafificin Alkhairi.

Rubutawa✍️✍️
ABUBAKAR NTA,
EDITOR “AREWA MEDIA WRITERS” TARABA STATE.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button