Rahotanni
Kada A Kuskura A kori Almajirai A Jahar Yobe~ Inji Gwamna Mai Mala Buni.
Daga Ahmad T Adam Bagas
Gwamnan Jahar Yobe Mai Mala Buni yace Kar a kuskura a kori almajiri koda daya ne a Yobe.
Buni yace shima ya tashi yaga mahaifinsa malamin Almajirarai ne kuma shi ma yayi karatun Alkur’ani mai girma tare da almajirai Sannan Yace Jahar su ta Yobe ta Samo asali ne Daga Almajirai da suke zuwa karatun Alkur’ani aka samu Jahar.
Mai mala yace duk Almajirin da aka Kawo daga wata Jaha Suna maraba dashi Yobe Jahar Sace Yace Sun Samamusu Wajen kwana da kayan more rayuwa ga Almajiran, Sannan suna Nazarin Za’a Gina musu Makarantun Kwana da Sauran Abubuwan da Suka dace Dasu Inji Shi.
Masu Karatu Me zakuce a kan wannan Batun Na Gwamnan Yobe???
Ahmed T. Adam Bagas