Rahotanni

Laifin manyan Arewa yasa aka kai Yunusa Yello Gidan Maza

Spread the love

Ko kunsan cewa sai da aka yi zaman kotu kusan sau biyar ba tare halartar lauyoyin dake kare shi ba?

Ko kuna da masaniyar cewa an nemi wasu manyan mutane su 3 daga jihar kano akan suje su bayar da sheda, wacce shedar tasu za ta iya sawa a bayar da belin Yunusan?… amma zuwan su ya gagara sabo da wasu matsaloli wadanda basu taka kara sun karya ba, kuma baza su gagare mu ba a matsayin mu na mutanen dake bibiyar case din..

Shin wai jama’a sun san da cewa tun farko sai da aka bayar da Belin Yunusa, ya dawo kano yaci gaba da harkokin sa, amma daga baya wasu mutane suka hadu suka Yaudare shi, suka turashi Jihar ta Bayelsa ya kai kan sa ga Hukumomi suka kamashi suka kulle a prison, kawai don su cimma burin su akan case din?

Wallahi fa Arewa muna da matsala… Bayan Matsalar shugabannin mu, mu talakawa mune babbar matsalar kawunan mu. Sabo da akan abun duniya zaka ga Talaka bai damu da ya jefa dan uwansa talaka cikin kowacce irin masifa ba muddin shi buqatar sa zata biya.
Allah ya sawaqe mana

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button