Rahotanni

Duk Wanda Ba Ya So A Kalubalanci Buhari Kan Kura-kurensa To Ba Masoyin Buhari Bane Na Kakika___Inji Mungadi.

Spread the love

Daga Kabiru Ado Muhd

Mungadi yayi wannan bayani ne yayin da yake maida martani ga wasu jiga jigai a gwamnatin Buhari, yayin da gwamnatin Buhari tasa aka kama Wanda ya jagoranci zanga zangar kin amincewa da kashe kashen da akeyi a arewacin Najeriya Ashir Sherrif.

Mungadi ya kara da cewa matukar baza a bar jama’a sufito su gayawa gwamnati gaskiyar abin da yake faruwa a tsakanin al’ummar da take mulka ba to tabbas daga wannan rana barna za ta cigaba da afkuwa.

Mungadi yace wadanda gwamnati ta wakilta don su binciko mata gaskiyar abin da ke faruwa acikin al ummarta sunki yin aikinsu tsakani da Allah, sun tsaya Kare kujerunsu, sannan kuma suna sawa anabi ana kame duk Wanda yagaji yafito yake fadar gaskiyar lamari.

Mungadi yace yana kira ga shugaba Buhari da yayi saurin tsayawa yasake tunani tun kan wankin hula yakai shi dare

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button