Duk Matsalolin Dake Damun ‘Yan Najeriya Laifin Manyan Jam’iyyar PDP Ne~Inji Comrade Mario.

Dalina na fadin haka shine duk kuncin rayuwar da ‘yan Najeriya ke ciki da tabarbarewar rashin tsaro da ciyowa Najeriya bashi mara dalili da wannan gwamnatin ta Buhari keyi manyan Jam’iyyar PDP sun zurawa abun ido basa daukar wani mataki, se dai maganganu marasa amfani a kafafen yada labarai.
Yau ana kashe ‘yan Arewa ana kidnapping, abun takaici manyan Jam’iyyar PDP sun zura ido, sedai wasu kungiyoyi ne ke kokarin hada zanga zangar nuna adawa da abinda ke faruw, jam’an tsaro suna kamasu ana kaisu a kulle, wanda manyan PDP yafi cancanta su jagoranci irin wadannan zanga zangar.
Yau in Atiku ne ya jagorancu zanga zanga kan nuna adawa da kashe kashen da ake a Arewa kuna ganin jami’an tsaro zasu kamashi?
Abu ne da baze yiwu ba, ai a baya da Buhari yana adawa shi yake jagoranta zanga zanga akan kudin fetur da gwamnati ta kara, Buhari ya jagoranci zanga zanga a Najeriya, sai ku ana kashe mutane kunsa ido wai kuna tsoron ku tanka ace kun siyasantar da harka tsaro.
Wacce irin siyasa kuke manyanmu na PDP?
Ina kishin Najeriyar naku yake?
Ina kishin talakan naku yake?
Kuna kallo ana kashe talakawan kasa kunsa ido sedai wasu kungiyoyi suyi, bayan kunsan kungiyoyin basu da karfin ikon yi kamarku.
Yau in akace Atiku ko shugaban PDP suna jagorantar wata zanga zanga akwai wani jami’in tsaro da zasu taho yace su juya koya kamasu?
Dan haka akwai lefin manyan PDP a abinda yake faruwa a Najeriya, dan sune zasu fito su jagoranci zanga zanga, dole a gyara, domin dokar kasa ta basu dama
A karshe ina kira ga jigogin Jam’iyyar PDP su fito su jagoranci wannan zanga zanga indai da gaske suna kishin Najeriya da talakawan Najeriya, domin dokar kasa ta baku dama, kowanne babba ya jagoranci ta jiharshi, wannan shine kirana gareku manyanmu na PDP.
Allah ya kawo mana zaman lafiya a kasarmu Najeriya Amin.
Daga Naku MARIO.