Siyasa

A ajiye maganar Siyasa ayi maganar Gaskiya, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnatinsa Sun Gaza ta Fuskar Samarda Tsaro, In ji wani Dan Majalissar Daga APC.

Spread the love

Matsalar Tsaro;- Dan Majalisar Tarayya Na APC a Neja Ya Caccaki Gwamnatin Buhari…

Dan majalisar wakilai, Mai wakiltar Karamar Hukumar Chancaga a Jihar Neja, Hon. Umar Muhammad Bago, ya Ce a Ajiye maganar Siyasa ayi maganar Gaskiya, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnatinsa Sun Gaza ta Fuskar Samarda Tsaro.

Bago, a zantawarsa da Sashen Hausa Na Rediyo RIF, yace “Alhakin tsaro Na kan shugaba Buhari kuma duk Wanda za’a Ambata a sha’anin Tsaro yana Kasan Buhari ne, kuma Gwamanati ta gaza Samar da tsaron nan.

“Wasu Tsirarun mutane suna yawo kan mashin suna Sacewa da kashe mutane, Ga Sojoji da Jirage Gwamnati tana da su amma an kasa Daukar Matin da ya dace.

“Ya kamata Gwamnati ta dauki matakin Share Dazuzzukan da wadan nan Yan’adda ke buya- Inji Shi.

Yaci gaba da Cewa ” Ya kamata gwamnati ta Ajiye kowanne Kongila da takeyi Na Aiki ta Fuskanci Sha’anin Tsaro, domin Tsaro na gaba da komai.

Wannan Dan Malisar kuma Jigo a Jam’iyyar APC ya fito fili ya Bayyana gazawar Gwamnati, duk da Wasu Shuwagabanni a Jam’iyyar Basa Fitowa suce gwamnati ta Gaza domin Suna ganin za’ace Jam’iyyarsu ce ta Gaza.

Ko’a makon da yagaba Saida Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kudancin Borno a Majalisar Dattawa Hon. Sanata Ali Ndume, Ya Ayyana cewar Wannan Gwamnatin Bada gaske Take Yaki da Boko Haram ba, Ganin Yadda Shugaba Buhari ya Sanya Biliyan 26bn, kacal a Kasafin Shekara me zuwa domin Samarda Tsaro a Kasar Nan.

Kuma Masana da dama Sun goyi bayan Ndume, Cewar 26bn. Tayi kadan Kan Tsaro a Kasar Nan.

Sunce ko a Shekarar 2014, Gwamnatin baya Ta Saka Triliyan 1ne a kasafin kudin Tsaro, lpkacin ma da Boko Haram Kadai ce Matsalar Kasar, kuma Naira Tanada Daraja a lokacin fiye da Yanzu.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button