Rahotanni

A fadar shugaban kasa ake tata iskanci na gaske kuma Buhari ne jagora__martanin Aisha Yesufu ga shugaba Buhari.

Spread the love

Yar gwagwarmaya kuma jagorar masu zanga zangar EnDSARS Aisha Yesufu tayi martani ga gargadin da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yayi ga masu yunkurin sake dawo da zanga zangar EnDSARS karo na biyu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi gargadi kan yunkurin sake bijiro da zanga zangar EnDSARS a wasu sassa na kasarnan, Buhari yace gwamnati bazata sake zubawa wasu ido su sake kawo musu wani iskan ci a Najeriya ba, kuma bazasu bar duk wani wanda zai shiga rigar masu zanga zangar lumana ya tayar da zaune tsaye ba.

Nan take Aisha Yesufu ta mayar da martani da cewa a fadar shugaban kasa ake tata iskanci na gaske kuma shugaba Buhari shine jagora, Aisha Yesufu ta mayarwa da shugaba Buhari martanin ne bayan yayi wannan gargadin a yau Litinin.

Daga Kabiru Ado Muhd.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button