Labarai

A gudanar da cikakken bincike kan dakatar da shugaban karamar hukumar shiroro ~ Majalisar Jihar Neja

Spread the love

Majalisar dokokin jihar Neja ta umarci kwamiti kan harkokin kananan hukumomi da harkokin masarautu da su binciki rikicin wanda ya haifar da dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Shiroro, Mista Sulaiman Dauda Chukuba, da bangaren majalisar dokokin jihar.

Wannan ya ƙkunshe ne a cikin wani kuduri, da Hon. Malik Madaki Bosso, memba mai wakiltar Mazabar Bosso ya ambata.

Madaki Bosso ya yi bayanin cewa, dakatarwar da Shugaban Karamar Hukumar, Mista Sulaiman Dauda Chukuba, ya haifar da mabanbantan ra’ayoyi daga jama’a, a wurin ta hanyar zargin mambobin Majalisar Dokokin jihar Neja da rura wutar rikicin .

“Bayan dakatarwar da aka yi wa Shugaban karamar hukumar Shiroro, wasu mutane suna ta zage-zage a kan wannan Majalissar Mai Girma, suna zargin mambobin ta da ruruta rikicin karamar hukumar Shiroro”, in ji shi.

Malik Madaki Bosso, ya ce dole ne majalissar mai martaba ta yi duk abin da doka ta tanada don kare mutuncin mambobin ta.

Daga nan sai majalisar ta umarci kwamitin majalisar kan harkokin kananan hukumomi da lamuran masarauta da su binciki rikicin karamar hukumar Shiroro sannan su kawo rahoto gidan kafin rana 25 ga Fabrairu, 2021.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button