Rahotanni
A Jahar Borno Har Yanzu Jama’a Basu Yarda Cutar Covid-19 Gaskiya Ce Ba. Inji Mataikamin Gwamna Umar Kadafur….
Daga Haidar H Hasheem Kano
Jaridar The Cable ta ruwaito, Umar Kadafur, wanda shine shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar Borno, ya kwatanta annobar da Boko Haram.
Ya ce yadda take kutsawa cikin jama’a na daidai da yadda mayakan ta’addancin Boko Haram ke shiga sassan kasar nan.
Yace duk da yadda take sake shiga wurare, wasu jama’a suna take dokar nisantar juna ta yadda suke zuwa jana’iza da kuma sallar jam’i.
Ya kwatanta lamarin da abun takaici.
A lokacin da Boko Haram ta fara, mutane da yawa suna tsammanin wasa ne, har sai da ta shafesu.
Wannan annobar wata nau’i ce irin Boko Haram kuma har yau wasu basu yadda da wanzuwar ta ba,” Kadafur ya sanar a wata takarda da ya fitar.