Rahotanni

A Jahar Katsina Ba Corona Virus Bace Matsalarmu, Yan Bindiga Dadine Matsalarmu. Inji Gwamna Masari.

Daga Haidar H Hasheem Kano

Gwamnan Jahar Katsina Aminu Bello Masari ya baiyana a shafinsa na Twitter cewa babbar matsalar da jaharsa take fuskanta shine barazana daga yan bindiga dadi.

Cikin saqon daya wallafa ya baiyyana akalla makwanni biyu da suka shude ansamu asarar rayukan mutane sama da 50, wanda duk hakan yafarune saboda ta’addancin yan Bindiga dadi.

Mutanen Kastina sunfi tsoran Yan Bindiga dadi fiye da wannan cutar ta Covid-19, duk da barazanar cutar ga Al’umma amma tabbas wannan matsalar tafi cin rayukan al’umma fiye da wannan annobar.

Gwamnan ya jaddada cewa sun rasa hanyar dazasu gamsar da al’umma kan abinda suke fadamusu a gameda halin da ake ciki

A karshe yayi kira ga ma’aikatar tsaro ta kasa dasu Kara jajircewa wajan ganin an tabbatar da zaman lafiya a fadin jahar baki daya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button