Lafiya
A Jahar Legas An Kara Samun Mutuwar Majinyata Biyu Masu Cutar Covid-19
Daga Haidar H Hasheem Kano
Rahotannin dasuke riskarmu a yanzu sun tabbatar mana da cewa cikin majinyatan an samu karin mutum biyu da suka rasu.
Hukumar lafiya ta Jahar Legas ta tabbatar da faruwar hakan, inda ta wallafa hakan a shafukanta na sada zumunta.
Yazuwa yanzu Jahar ta Legas itace kan gaba wajan masu dauke da kwayar cutar ta Corona Virus, kuma sune sukafi kowacce jaha adadin wadanda suka rasa rayuwarsu a yayin da ake fama da wannan Annobar
Hukumar ta baiyyana cewa tana iya bakin kokarinta wajan ganin ta baiwa Majinyatan cikakkiyar kulawar data dace a lokacin jinyar tasu, inda cikin masu jinyar wasu nasu yayi tsanani hakan ke janyo asarar rayuka.