Lafiya
A Jahar Yobe Ma Ana Samun Karuwar Mace-mace…

Daga Haidar H Hasheem Kano
Jaridar Sahara Reporters ta buga wani rahoto da ke cewa a cikin kwanaki shida kadai an yi mace-macen mutane 155 a cikin garuruwan Gashua, da Potiskum, tare da ganin alamun cutar corona da mamatan.
Rahoton jaridar ya kara da cewa; mace-macen da ake gani a jahar ta Yobe, sun yi kama da irin wadanda su ke faruwa a jahar kano, a arewacin kasar, wacce hukumar fada da corona ta tabbatar da cewa da akwai alamun cutar tare da wadanda su ka mutun.
A garin Potuskum an sami mutuwar mutane 98 daga ranar 30 ga watan Afrilu zuwa 5 ga watan Mayu, kamar yadda wata majiya ta tabbatarwa da jaridar ta Sahara Reporters.
A garin Gashua kuwa mutane 57 ne su ka kwanta dama, mafi yawancinsu dattijai ne.