A jihar katsina wani Uba Ya dage Sai ya yi wa ‘yarsa mai shekaru Sha uku 13 Auren dole ga abokinsa dan shekara tamanin 80.
Roƙo Da Kira Ga Dikko Akan Yunƙurin Auren Dole Ga Ƴar Shekara 11 Ga Wani Dattijo Mai Shekaru 80 A Unguwar Rahmawa
……Guri na inyi karatun addini da na boko, ba auren tsoho mai shekaru 80 ba – Inji Sayakulu
Ƙungiyar Dikko Young Foundation and Development Society ta nuna damuwa matuƙa tare da yin kira ga Gwamna Dikko Umar Raɗɗa da sauran hukumomi da masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani kan yunƙurin auren dole da wani Uba mai suna Malam Umar dake zaune a Unguwar Rahmawa Ƴan hura-hura, ke shirin yiwa ƴar sa ta cikin sa mai shekaru 11 ga wani abokin sa dattijo mai shekaru 80.
Yarinyar wadda Mahaifin nata gaba ɗaya a rayuwar ta bai sanya ta karatun boko da karatun addini ba, ya yanke shawarar auren dole gare ta zuwa ga abokin sa tsoho mai shekaru 80, wadda yarinyar ta nuna bata son sa, tare da yunƙurin guduwa ta bar iyayen ta.
Shugaban Ƙungiyar Ambasada Ahmed Aminu ya bayyana hakan tare da wannan kiran a lokacin da ya ke zantawa da Kafar sadarwa ta Katsina Post, a Unguwar Rahmawa kwanar ƴan hura-hura a cikin birnin Katsina.
A cewar sa, ya samu wannan mummunan labarin guduwa da ƙaramar yarinyar ke shirin yi daga bakin wata mata mai suna Ummi Yahaya Rahmawa da ta hana yarinyar guduwa tare da taimakon ta, da bata abinci da kayan sawa.
Ya bayyana cewa tuni uban ya yanke shawarar ba zai bar yarinyar ta fara jini a gidan sa ba, akan zargin da ya yi cewa yarinyar ta faɗa masa wai zai karya mashi wani asiri nasa, a saboda haka ya yanke shawarar aurar da’ita nan da kwanaki ƙasa da 20 masu zuwa.
Ambasada Ahmed Aminu wanda ya bayyana damuwa kan yiwuwar cutar yoyon fitsari ya kama yarinyar idan aka aurar da ita a waɗannan ƙananan shekaru, ya yi kira ga Gwamna Dikko Raɗɗa da Kwamishiniyar harkokin mata data shigo ta kawo ɗauki kan wannan lamari.
Yace Shugaban Ƙungiyar Gwagware Foundation Yusuf Aliyu Musawa tuni ya sha alwashin ɗaukar nauyin karatun yarinyar idan har uban ta ya amince ya fasa aurar da’ita, inda kuma tuni Gwamna Raɗɗa ya bada umarnin a hana wannan ɗanyen aikin.
A lokacin da aka zanta da yarinyar Sayakulu Umar wadda ke ta rusa kuka kan halin da ƙaƙanikayi da uban ta ke shirin jefa ta, tace Mahaifin ta Malam Umar bai taɓa sanya ta makarantar boko ko addini ba, wanda gurin ta shine tayi ilimi ba aure ba da waɗannan ƙananan shekaru 11.
Sayakulu Umar ta kuma bayyana wa Katsina Post cewa, ko Mahaifiyar ta Fatima Mamman bata da ra’ayin a aurar da’ita ga wannan sa’an Mahaifin ta, amma ta amince mata don bata da yadda zata yi.
Ta ƙara dacewa, Mahaifin ta ya yi rantsuwar tsine mata idan bata amince da auren ba, wanda ya sanya ta yanke shawarar tafiya cikin duniya, akan tayi auren dole, amma wata baiwar Allah mai suna Ummi Yahaya ta hana ta.
Sayakulu Umar ta yi kira ga Gwamna Dikko Raɗɗa da hukumomi da su kawo mata ɗauki, sannan su taimaka mata ta cimma gurin ta ɗaya tilo na yin ilimi.
Katsina Post