A jihar Kebbi Matasa Sun kashe matashi Kan dubu uku N3,000 Kacal.
Sharifuddeen Sale Kanya da yake matakin karshe (400L) a jami’ar kimiya ta jihar Kebbi dake Aliero ya gamu da ajalinsa, inda wasu suka kashe shi jiya bayan cinikin wayar selula.
Rahotanni sun nuna cewa bayan ya tura musu kudi 3500, suka ba shi wayar, bayan ya koma makaranta ne ya ga banki sun dawo masa da kudin, sai ya koma don ya ba su kudinsu, shine suka rufe shi da duka suna ihu barawo, suka yi masa dukan kawo wuka, ya samu karaya biyar da munanan raunuka.
Daga baya aka garzaya da shi asibiti amma daga karshe ya amsa kiran Ubangiji Mahalicci.
Rahotanni sun nuna cewa a dazu daliban jami’ar sun gudanar da zanga-zanga, inda ya kai ga rufe makarantar har illamasha Allah.
Daga karshe muna neman gwamnati ta dauki kwararan mataki don ganin an hukunta duk wanda keda hannu a faruwar lamarin. Daga Mustapha Alhassan Gwazawa