Rahotanni
A kalla Mutane 6 Da Motoci 7 Ne Suka Kone Sakamakon Hatsarin Tankar Mai A Neja.
Da Safiyar Yau Dinnan ne Wata Tankar Mai Ta Kama da Wuta bayan Sunyi Taho mu Gama da Wata mota a Karamar Hukumar Lapai ta Jihar Neja.
Lamarin Da Yayi sanadiyyar Rasuwar Mutane 6 da dama Kuma Sun Jikkata, Motoci 7 Kuma Sun kone Kumus.
Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya Jajan tawa Iyalan Wadanda Suka Rasa Ransu sanadiyyar Hatsarin Inda Yayi Addu’ar Allah Ya musu Rahama, Ya Kiyaye Gaba.
Hatsarin dai ya Afkune Sanadiyyar Rashin kyan Hanyar da Ta Hada Karamar Hukumar Bidda, Agaie, Lapai da Garin Lambata duk a Jihar Neja.
Allah ya Kyauta…..
Ahmed T. Adam Bagas