Tsaro
A Karo Na Biyu Boko Haram, Sun kai hari Kan Tawagar Zulum Yau.
A yau juma’a ne Mayakan Boko Haram Suka kai harin kan tawagar Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, a kan Hanyarsa daga Maiduguri zuwa Manguno a Jihar.
Abin ya farune a dai dai garin Korochara, Inda gwamnan zai Halarci garin Manguno Inda Za’a Kwashe ‘Yan Gudun Hijira guda dubu daya domin mai dasu garinsu Na Asali Baga.
‘Yan sanda guda 8 da sojoji guda 3 da yan kato da Gora guda 4 ne suka rasu a harin, sai kuma wadanda suka samu munanan raunuka.
Kawo yanzu bamu sami cikakken bayani game da lafiyar gwamnan ba.
Daga Ahmed T. Adam Bagas & Kabiru Ado Muhd.