Labarai

A kokarin sa na sasantawa da ‘yan ta’adda Sheikh Gumi zai ziyarci Garin kagara inda aka sace dalibai a Jihar Niger.

Babban malamin addinin Islama, Sheik Ahmad Gumi, ya yi alkawarin ziyartar al’ummar Garin kagara Dake Jihar Neja, inda aka sace wasu mutane a safiyar ranar Laraba.

An sace wasu dalibai da ma’aikatan Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kagara, hedikwatar karamar Hukumar Rafi da ke Jihar Neja da sanyin safiyar Laraba.
Da yake jawabi bayan ziyarar da ya kaiwa gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, Gumi ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa jihar Kebbi amma ya yanke shawarar tsayawa a Minna, babban birnin jihar Neja, don samun damar ganawa da Gwamnan kan lamarin satar mutane.

Shehin malamin ya ce wannan shi ne karon farko da zai ziyarci Nijar, ya kara da cewa tattaunawar da zai yi da Gwamnan shi ne ba gwamnati damar samar da mafita kan rashin tsaro.

“Ni da Gwamna mun yi magana a kan hanyoyi da yawa don magance rashin tsaro ta hanyar da ta dace da kuma nemo hanyoyin magance matsalar rashin tsaro a jihar,” in ji shi.

Makonni biyu da suka gabata, Gumi ya sadu da ‘yan fashi a maboyarsu, yana roƙonsu da su rungumi zaman lafiya.

Daga baya ya nemi Gwamnatin Tarayya da ta Jiha da su yi afuwa ga ‘yan fashi, yana mai cewa tattaunawa ita ce mafita ga rashin tsaro.

Amma wasu masu ruwa da tsaki, ciki har da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, sun yi watsi da shawarar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button