Lafiya
A Kowacce Rana Mutane 50 Ne Ke Kamuwa Da Cutar Kanjamau A Jihar Adamawa NEPWHAN
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Rahotanni sun bayyana cewa a kullun ta Allah mutane 50 ne ke kamuwa da cutar Kanjamau a jihar Adamawa.
Hakan ya fito ne daga shugabar kungiyar mutane masu rayuwa da cutar reshen jihar Adamawa, NEPWHAN, Farah James.
Tace akalla mutabe Dubu 36 ne ke amfana da magungunan yaki da cutar da ake rabawa a jihar.
Da take magana a wajan wani shiri na hukumar majalisar dinkin Duniya dake kula da masu cutar, USAID Farah tace yawanci mutane na kamuwa da cutar a jihar ba tare da sun sani ba.
Tace kuma babbar matsalar shine yawancin mutane da suka shiga hadarin kamuwa da cutar basa zuwa ana gwadasu saboda gudun kada a ce suna da ita.