A Lokacin Buhari yayi alkawarin zai Gama da Boko Haram ne a Matsayin Dan adawa ba Jami’in Gwamnati ba ~Adesina
Femi Adesina Mai Magana da yawun Shugaba Kasa ya bayarda amsa a Lokacin da aka tambaye shin ko Buhari ya iya kawar da Boko Haram kamar yadda ya yi alkawari lokacin kamfen dinsa? Sai Adesina ya ce dole ne a bayyana cewa Shugaban ya yi wasu alkawura ne a matsayin dan adawa ba jami’in gwamnati ba.
Don an ci karfin ‘yan ta’addan ta hanyar fasaha amma har yanzu suna aiki a wasu yankuna a wani karamin mizani.
Adesina ya lura cewa Shugaban kasar ya fada a makon da ya gabata cewa hukumomin tsaro sunyi Abu mafi dacewa da kyau
Mai taimaka wa shugaban kasar ya kuma yi tir da ikirarin da tsohuwar Ministar Ilimi, Oby Ezekwesili ta yi, cewa sacewa da ceto fiye da ’yan matan makarantar Kankara 300 da abin shakku ne ga da aminta.
Daga Karshe Adesina ya ce amincin gwamnatin Buhari tana nan daram.