A shirye nake in ci gaba da daukar tsauraran matakai don ciyar da Najeriya gaba – Tinubu
Shugaba Bola Tinubu, a ranar Juma’a a nan birnin Beijing, ya ce a shirye yake ya dauki matakai masu tsauri don ciyar da al’ummar kasar gaba, yana mai cewa ba abu ne mai sauki ba a koyaushe shugaba ya samu fahimtar juna kan al’amura.
Shugaban ya bayyana cewa, a lokacin da ya gana da ‘yan Najeriya mazauna jamhuriyar jama’ar kasar Sin domin kammala ayyukansa a kasar.
TInubu ya bayyana ziyarar tasa a matsayin “mai kyau da nasara”.
A yayin da yake jawabi ga mambobin kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje a kasar Sin, NIDO China, da al’ummar Najeriya a otal din China World, Shugaba Tinubu ya jaddada kokarinsa na karfafa hadin gwiwa a fannonin samar da ababen more rayuwa, kasuwanci, kudi, makamashi, tattalin arzikin kore, da ma’adanai yayin tattaunawarsa da shugaban kasar. Xi Jinping, firaministan kasar Li Qiang da halartar taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) na shekarar 2024.