A yau ne EFCC za ta gurfanar da tsohon Gwamna Bello a gaban kuliya bisa zargin karkatar da kudi N80.2bn
Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Adoza Bello a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis, 18 ga Afrilu, 2024.
Za a gurfanar da shi a gaban mai shari’a Emeka Nwite tare da wasu mutane uku Ali Bello da Dauda Suleiman da kuma Abdulsalam Hudu a kan tuhume-tuhume 19 da suka hada da karkatar da kudaden da suka kai N80,246,470,088.88.
Gurfanar da Bello ya biyo bayan sammacin kamawa da hukumar EFCC ta nema a kotun a ranar Laraba, 17 ga Afrilu, 2024.
A cewar Dele Oyewale, mai magana da yawun hukumar EFCC, “ Yunkurin hukumar na aiwatar da umarnin kama Bello bisa doka ya gamu da turjiya a ranar Laraba, 17 ga Afrilu, 2024. Gwamna mai ci yanzu ne ya keta ka’idojin tsaro a gidan tsohon gwamnan a Abuja, Gwamnan na jihar Kogi, Usman Ododo ya tabbatar da cewa wanda ake zargin an dauke shi a motar sa.
“A matsayinmu na hukumar da ke da alhakin tabbatar da doka, EFCC ta yi haquri a kan tunzura ta, tana jiran a gurfanar da shi a ranar Alhamis, 18 ga Afrilu, 2024.
“Ya zama dole a bayyana cewa Bello bai fi karfin doka ba kuma za a gurfanar da shi gaban kuliya da wuri,” in ji shi.