Abba Bichi ɗa ga shugaban ‘yan sandan sirri na SSS ya yiwa matar Ned Nwoko ruwan kuɗi.
Yayin da ’yan Najeriya ke kokawa kan matsananciyar yunwa da karancin kudin Naira, Abba Bichi, dan babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (SSS), Yusuf Bichi, ya fito a cikin wani faifan bidiyo da yana lika tarin sabbin takardun kudi ga Matar Nwoko, Regina Daniels.
An gan shi yana likawa Ms Daniels sabbin takardun Naira a cikin faifan bidiyon da ake kyautata zaton an nade shi ne a wani gidan rawa da ke Abuja babban birnin kasar, matakin da ya saba wa manufar babban bankin Najeriya, wanda ya haramta likin Naira. .
Mista Bichi, wanda ya yi suna wajen nuna dukiya a shafukan sada zumunta, ya sha suka daga masu amfani da yanar gizo kan yadda yake nuna dukiyarsa a bainar jama’a, musamman a shafin Instagram, inda ya ke da mabiya.
Nuna arzikinsa ya kasance abin tattaunawa ga jama’a, la’akari da matsayin mahaifinsa a matsayin shugaban ‘yan sandan sirri na kasa.
Wannan na baya-bayan nan ya zo ne a daidai lokacin da wasu abokan cinikin banki ke koke-koke game da karancin takardun kudi na Naira a kantuna, Automated Teller Machines (ATMs), Points of Sale (PoS), da Bureaux de Change (BDCs). Haka kuma wasu jami’an bankin Deposit Money sun yi ikirarin cewa ba sa samun isassun kudade daga bankin CBN a lokacin bukukuwan.
Koyaya, babban bankin ya yi iƙirarin cewa akwai isassun kuɗin.
Karancin kudin Naira na kara kara wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta, wadanda tun daga lokacin suka fara kokawa da tasirin manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu.
Hakan ya bayyana ne a wani faifan bidiyo na mazauna tsibirin Legas suna ihun “Muna jin yunwa” a yaren Yarbawa yayin da ayarin shugaban kasar ke wucewa a ranar Juma’ar da ta gabata.
Peoples Gazette