Rahotanni
Abba Gida Gida ya bayyana kadarorin da ya mallaka..
Zababben gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif ya bayyana a hukumar da’ar ma’aikata.
Abba Gida Gida ya bayyana kadarorin nasa ne a wani kundi da ya mikawa hukumar da’ar ma’aikata, duka a shirinsa na karbar ragamar mulkin jihar Kano.
Ya bayyana a shafinsa na twitter kamar haka:-
“Alhamdulillah, A yau na bayyana kadarorina a cikin wani kundi da na gabatarwa hukumar kula da ɗa’ar ma’aikata ta ƙasa reshen jihar Kano (Code of Conduct Bureau)
A yayin da mu ke jiran gabatowar ranar 29 ga watan Mayu don karɓar rantsuwa, wannan bayyana kadarorin zai kasance wata…