Labarai

Abba Gida-Gida ya jaddada aniyarsa ta rushe duk wani filin makarantu da makabartu da Gwamnatin Kano ta Sayarwa mutane.

Zababben gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya jaddada maganar sa ne a shafinsa na Facebook yaka Mai cewa Kamar yadda muka kuduri aniyar dawo da tsarin birnin Kano;  Ina shawartar Jama’a da su daina duk wani aikin gine-gine na filayen gwamnati a ciki da wajen makarantu, wuraren addini da na al’adu, da dukkan asibitoci, da makabarta, da kuma gefen katangar birnin jihar Kano.  – AKY

Daman dai Abba Gida-Gida ya Sha alwashin rushe duk wani filin Gwamnati wanda Gwamnatin Kano Mai ci yanzu ta sayar ake gine gine a halin yanzu.

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Ganduje ta shahara wajen yankawa da sayar da makarantu makabartu masallatai asibitoci wanda suke mallakin Gwamnatin jihar ne.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button