Labarai

Abba Gida Gida Ya Maka Ganduje A Kotu.

Spread the love

Dan takarar gwamnan jihar Kano a zaben shekarar 2019 karkashin Jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusif yayi Karar gwamnatin Kano da kuma ‘Dan Kasuwar nan Mudassir and Brothers da kuma ELSAMAD a gaban Kotu.

Abba Kabir ya shigar da karar ne inda yake kalubalantar gwamnatin Kano kan matakin data dauka na baiwa Muddasir and Brothers tsohon Otal din Daula da kuma Tashar Mota ta Shahuci domin yin Kantin Zamani.

Lauyan Abba Kabir Barrister Bashir Yusuf Tudun Wuzurchi yace mika wuraren ga wani mutum guda kawai ya saba da bukatu ko muradin Talakawa har ma da dokokin kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button