Labarai

Abba Sadau yayan Jaruma Rahma Sadau zai Angwance.

Spread the love

Haruna Ibrahim Sadau, wanda ake kira Abba Sadau, shi ne babban wan su fitacciyar jaruma Rahama Sadau. A jiya Juma’a, 15 ga Janairu, 2021, Abba ya bayyana sanarwar cewa za a yi bikin auren sa a ranar 30 ga wannan watan, kuma ya na gayyatar kowa da kowa. A wani saƙon musamman da ya tura a soshiyal midiya, Abba, wanda furodusan finafinai ne a Kaduna, ya haɗa har da hotuna shida na kyakkyawar yarinyar da zai aura, waɗanda su ka ɗauka a situdiyo, wato abin da ake kira ‘pre-wedding pictures’.

Ganin wancan saƙo na Abba Sadau sai mutane su ka shiga yi wa kan su tambayoyi: Shin wace yarinya ce wannan Abba zai aura? Ya sunan ta? ‘Yar ina ce? Wane yare ce?

Kai, akwai ma masu yin tambayoyi a kan shi kan sa angon, musamman waɗanda ba su san shi sosai ba, su na faɗin shi Abban da gaske wan Rahama Sadau ne ko dai ƙanen ta ne? Shi ma ɗan fim ne? Idan wan Rahama da ƙannen ta mata ukun nan da ake gani ne, me zai ce game da auren waɗannan tsala-tsakan ‘yanmatan? Me ya sa har yanzu Rahama ba ta yi aure ba?

Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin zantawa da Abba Sadau don samun amsoshin waɗannan tambayoyin, ciki har da yadda za a yi bikin a cikin wannan yanayi da ake ciki na cutar korona da kuma dalilin da ya sa ya riga ƙannen nan nasa yin aure. Ga yadda hirar ta kasance:

FIM: Da farko, za mu so ka faɗa mana cikakken sunan ka da tarihin rayuwar ka a taƙaice.

ABBA SADAU: Da farko dai suna na Haruna Ibrahim Sadau, wanda aka fi sani da Abba Sadau. An haife ni a Kaduna, na yi firamare da sakandare duk a Kaduna, sannan na yi jami’a a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua da ke Katsina. Na fara bautar ƙasa a Jihar Osun, daga baya na nemi dawowa Kaduna, inda a nan na ƙarasa. Kuma ni yaya ne ga jaruma Rahama Sadau.

FIM: Ga shi auren ka ya matso kusa. Yaya sunan amaryar taka?

ABBA SADAU: Sunan ta Zainab Musa Yarima, ana kiran ta da Zee Yarima.

FIM: ‘Yar wane gari ce? Kuma Bahaushiya ce ko ta na da wani yaren?

ABBA SADAU: ‘Yar nan Kaduna ce. Bahaushiya ce, amma su na da dangantaka da Maiduguri. Amma dai duk a nan Kaduna aka haife su. Kuma mun daɗe tare, aƙalla mun kai shekara takwas tare.

FIM: Me ku ka shirya yi a bikin?

ABBA SADAU: To, saboda wannan abu da ke ta faruwa na korona da sauran su, ka san Kaduna akwai doka an hana taruka da sauran su. Amma yanzu dai abin da mu ka shirya, idan aka ɗaura aure, daga wurin za mu wuce Sadauz Home a yi walima. Sai kuma mu na tunanin yin dina, in dai Gwamna ya bada damar a ci gaba da taro, tunda an ce 18 ga wata za a saki gari, za a koma makaranta, za kuma a ci gaba da ɗakunan taro, amma sai da takunkumi da sauran su. In dai ya yiwu sun buɗe ‘hall’ ɗin sun fara karɓar kuɗi, sai mu je mu biya mu yi dina, in-sha Allahu.
ABBA SADAU: To, shi wannan maganar da ma mun daɗe mu na yin shi. Kuma ka san da ma ‘ya’ya mata sai an bi a hankali, sannan duk burin uwa da uba su ga cewa sun aurar da su. A kan haka ne mu ka zauna mu ka yi mitin da ‘family’, sai aka ce, “Tunda kai ne babba, ka fara buɗawa, sai mu ga abin da Allah zai yi. Ka ga daga kan ka, in ka yi, su kuma sauran – tunda da ma da na gaba ake koyi – sai su yi.”

Wannan mitin da mu ka yi da ‘yan’uwan baban mu da sauran su kenan, su ka ce ni in fara yi. Kuma da ma ita yarinyar (Zainab), kowa a ‘family’ ya san mu tare. Nan na yarda, na ce, “Ba damuwa, ni zan fara yi.”

Da maganar da saka rana duk a cikin watan Disamba aka yi, na ce a saka wata ɗaya kawai, kada abin ya yi nisa. Ka ga daga nan sai in buɗe masu ƙofa, sai kuma mu ga abin da Allah zai yi, wataƙila ma Allah ya sa dukkan su a lokaci guda za a yi bikin nasu.

FIM: Kai ma ka na ɗan taɓa harkar fim ne?

ABBA SADAU: E to, da dai ina yi, amma daga baya-bayan nan na zo na ja jiki. Saboda wasu ‘yan dalilai da su ke faruwa sai na ga gara na daina, na cire duk wani abu na harkar fim. Duk na cire. Har a Instagram na goge duk wani abu da ya shafi harkar fim da na ɗora.

Amma a baya na yi. Duk wani fim da Rahama ta yi, ni ne furodusan shi, tun daga kan ‘Rariya’, ‘Ɗan-Iya’, ‘Mati A Zazzau’ duk mu mu ke yin komai; ita ce dai furodusa amma ba ta san abin da ake yi ba, ta na bacci, sai mu ce mata an yi kaza da kaza. Da ma da ni da Yunusa Mu’azu ne mu ke yi.

FIM: Amma ka na ganin nan gaba za ka koma?

ABBA SADAU: Gaskiya ba na tunanin komawa, na daina. Gara na ci gaba da bizines ɗi na can daban kawai, saboda na ga harkar fim ɗin ne yanzu sai a hankali, ba layi na ba ne gaskiya. Kuma ba zan iya ba. Akwai abubuwa da dama da ke faruwa wanda ba zan iya jurewa ba. A nan gaba idan aka ci gaba da haka za a iya samun matsala da ni. Ina da haƙuri sosai, amma in na fusata ba daɗi! Don haka hanyar lafiya a bi ta da sauƙi.

Kuma ban taɓa faɗa da kowa ba a industiri, kowa nawa ne. So, harkar fim ɗin ne ta koma sai kame-kame ake yi, shi ya sa na ga bari in je in nemi wata sana’ar kawai. Na ga ina da digiri, kawai bari in je in ci gaba da buge-buge na tunda na san hanyoyin kasuwanci iri-iri.

FIM: Abba, mun gode. Daga FilmMagazine

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button