Abinda ke bata mana rai shine Kirista ya ginawa Almajirai Makarantun Allo musilmi Kuma Yana rushewa ~Inji Sheikh Dahiru Bauchi.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi a wani gajeran bidiyon ya fito ya Caccaki Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari Kan da wasu Gwamnoni Kan Kama Almajiransa Shehun Malamin Ya bayyana Cewa kowanne Dan Nageriya Dan Nageriya Yana da ‘yan cin Zama a ko’ina a Nageriya to maye Kuma ya kawo Maganar komawa da Almajirai gidajensu? Suma masu karatun Alkur’ani ‘Yan Nageriya suna da ‘yan cin Zama a ko’ina a Nageriya
Sanin darajar Alkur’ani yasa ake Almajiranci Muna addu’a Allah ya taimakemu Inji Shehun malamin.
Shehun malamin ya Kara da Cewa Kuma Abinda yake Bata Mana rai shine ana yayatawa Cewa ga Wasu Gwamnati sunyi Mulki sun wuce sun ginawa gardawa ko tsagaya Makarantu Amma shugabansu ba musilmi bane Mai ikonsu ba musilmi bane
Sai Kuma aka samu wata Gwamnatin Shugabansu Musilmi ne yawancin masu ikonsu musilmai ne Kuma a mulkinsu ya zamana wuraren da aka Tara Almajiran yanzu sai jakuna Kuma an zuba Wasu marasa Galihu maimakon dakunan karatun Alkur’ani wannan shine yake Bata Mana rai Inji Shehun malamin…
Dukda Cewa Shehun malamin Bai Kama suna ba Amma dai maganarsa Bata Rasa nasa ba da dirar mikiyar da Gwamnatin Jihar kaduna tayi a Kan Almajiran sa ta kwashesu Cikin dare da zummar kubutar dasu daga kamuwa da cutar CoronaVirus a satin Daya gabata..