Al'adu

Abubuwa 7 Game Da Rayuwar Margayi Umaru ‘Yar Adua: Shine Shugaban Da Yafi Wowanne Shugaba Yawan Halartar Sallar Jana’iza Tun Daga Shekarar 1960 Zuwa Yanzu.

Spread the love

Daga Mutawakkil Gambo Doko

1- Marigayi Umaru Musa Ƴar adua shine farkon wanda ya fara bayyana adadin dukiyar daya mallaka a tsakanin gwamnonin Najeriya a tarihi, a loƙacin dayake a matsayin gwamnan jihar Katsina a shekarar 1999.

1- Marigayi Umaru Musa Ƴar’adua shine shugaban dayafi kowanne shugaba a tarihin Najeriya yawan halartar sallar jana’iza tunda daga shekarar 1960. Marigayin ya kan soke duk wani taro domin ya halarci sallar jana’iza

3- Marigayi Umaru Musa Ƴar’adua shine zaɓaɓɓen shugaban Najeriya na farko daya fara rasuw a Aso rock a tarihin ƙasar

4- Harwayau, Marigayi Umaru Musa Ƴar’adua shine shugaba na biyu ( mulkin soja da farar hula) daya rasu a Aso Rock bayan Marigayi General Sani Abacha

5- Marigayi Umaru Musa Ƴar’adua shine ya rage harajin VAT zuwa kaso %5 daga kaso %10 da Shugaba Olusegun Obasanjo ya ƙara

6-Marigayi Umaru Musa Ƴar’adua a loƙacin gwamnatinsa ne ya rage farashin man fetur daga ₦75 zuwa ₦65

7- Marigayi Umaru Musa Ƴar’adua shine yayi abin da ake kira 7Point Agenda a tarihin siyasar Najeriya .

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button