Sana'o'i

Abubuwa Goma Da Dole Sai Ka Daina Tsoronsu Kafin Ka Fara Sana’a.

Spread the love

Mene ne marabar wanda yanzu haka a lokacin nan da nake wannan rubutun yake samun riba, yana mayar da canji cikin aljihu da ragowar, ku wadanda kullum zaku tashi daga bacci sannan ku koma ku kwanta da dare ba tare da samun ko kwandala ba?

Tsoro.

Ko sau nawa mai son yayi sana’a ya tabbatar wa kanshi abunda yake da niyyar yi. Karanta wadannan abubuwa goma da duk wani mai so ya fara sana’a yake tsoro da hanyar shawo kan su.

  1. RASHIN SANIN DAGA INDA ZA A FARA.

Yawancin masu so su fara sana’a, basu san daga inda zasu fara ba bayan yanke shawarar hada-hadar da suke son yi. Ka fara da neman wani wanda ya cimma sak irin burin da kake son cimmawa.

Yi bincike akan wannan mutum, da irin kasuwancin sa sannan ka tuntubi shi ka gani ko zai iya baka shawara da bayanai. Idan bashi da lokaci ko sha’awar yayi maka magana, to zaka gane cewa ya samu nasara, kuma kaima zaka iya.

Ka cigaba da gashi sannan kayi abunda ya fi mayar da hankali, kana cigaba da tafiya, hanyar na kara maka haske.

  1. RASHIN KWAREWA.

Ta yiwu ka san abubuwa da yawa akan hajjar ka ko sana’ar ka domin amsa duk wasu tambayoyi da kwastomomi zasu yi maka, da ma warware musu duk wasu matsaloli da ka iya tasowa. Saboda haka kar ka damu kanka idan kana ji kamar baka son komai a wannan fannin ba.

Dangane da abubuwan da baka sani ba, zaka iya samo amsoshi. Babu kunya wajen neman ilimi. Maganar gaskiya, wannan abu ne ma da ya kamata ka ringa yi kullum idan kana so ka cigaba, komai girman sana’ar ka. Baza ka taba dena koyo ba: Ka saka rigar kwararre sannan ka sadaukar da kanka wajen tabbatar da sana’a mai burgewa.

  1. ANA MAKA KALLON MARA HANKALI.

Mutane da yawa zasu yi maka kallon mara hankali a lokacin da kake fara sabuwar sana’a, kuma gaskiya suka fada. Abu mafi sauki na yi shine kar ka taba daukar kasada, ka je ka yi ta yi wa wani aiki har karshen rayuwar ka.

Ya ka ji a ranka dangane da abun da na rubuta yanzu? Saboda kai dan kasuwa ne, kuma kasada a cikin jinin ka yake. Baza ka iya rayuwa babu shi ba.

Dole a yi maka kallon mara hankali mana a lokacin da za a ga fara abu karami, kawai kayi imani da baiwar da Allah Ya baka, kuma ka jawo hankulan ragowar mutane domin suma suyi imani da shi. Ka rungumi rashin hankalin ka, kuma ka kaunace shi saboda wadanda ake kira marasa hankali sune suke yin arziki da suna a duniya.

  1. RASHIN JARI

Fara kasuwa zai yi matukar sauki idan duk wanda yake da shawara zai iya shiga cikin banki kai tsaye a bashi kudi ko ya samu wanda zai bashi jari. To saboda wannan duniyar ba mafarkin ka bane, mai so ya fara sana’a ba tare da jari ba, dolen dole su fara ko ta halin qaqa.

Ba a farko baka da jarin da kake bukata, nan bada jimawa ba zaka gane cewa farawa sannu a hankali ba tare da komai ba yafi. Nima da N1,500 na fara a watan Maris din 2016.

  1. BA A YARDA DA KAI BA

Ko kana shakkar cewa mutane zasu mayar da hankali akan sana’ar ka saboda takardun ka ko jinsin ka, ko launin fatar ka, kai dai ka dauki ciniki da muhimmanci sannan ka faranta wa kwastoman rai.

Mutane zasu iya yanke shawara saboda siffar ka, amma babu wanda zai gardama da kwarewa da hazaka. Ko a farko babu wanda ya yarda da kai, a hankali mutane zasu fahimta kuma zasu yi imani da yadda kake gamsar da duka kwastomomin ka.

  1. RASHIN SAMUN KWASTOMOMI

Akwai matukar fargaba a lokacin da kake tallata wa duniya baiwar ka ko sana’ar ka a karo na farko, kana damuwa ko za a darajanta shi ko sabanin haka. Sai idan ka fara kasuwancin ka ne a lokacin da dama kana da mutane da yawa da suka san ka, kuma suka amince da kai shine zaka ga an fara baka kudi, in ba haka ba, to wallahi baza ji an cika maka inbox ko WhatsApp da sakonni ba.

Idan ka tunkari kasuwanci cikin nishadi da raha, akai akai kana cika alkawura, to babu shakka zaka ga canji a dan lokaci. A halin yanzu, sai ka dage wajen tsara yadda zaka ringa yin talla, sannan kayi nazari domin kara kwarewa wajen sanin sana’ar, kuma kayi wa kanka adalci saboda ka kai inda jama’a da yawa basu kai ba.

  1. RASHIN SANNIN YADDA ZAKA RIKE SANA’AR BAYAN KAYI NASARA

Gazawar rashin samun kalubalen da kusan duka masu fara sana’a suke fuskanta shine gabatar da sana’ar da duniya ta dade tana jira.

Yi tunanin da ka kawo kaya ko ka bude shago, mutane sun yi layi suna son ganin ka ko kayan ka. Shin wannan abun baya razana ka? Kana tsoron samun nasara ne, ko fargabar rashin iya biyawa kowa bukata?

Ba kai kadai bane. Samun nasara na jawo kadaici, amma dole sai an samu wani a sama domin gabatar wa duniya abunda take bukata.

  1. SAKA IYALINKA DA ‘YAN GIDAN KU A WANI HALI

A lokacin da kake fargabar cewa wannan sabuwar sana’a baza ta iya biya wa iyalanka bukatun su ba, ko za a iya shan kunya, to idan wani ya gaya maka cewa iyalanka da ‘yan gidanku suma suna bukatar wannan horo domin kara dankon zumunci da iyali? Matar ka ko mijin ki, ko iyaye na bukatar baka kafadar hutawa.

‘Ya’yan ka zasu so su ga ka sayo wannan motar ko ka gina wannan gidan da kake ta so. Saboda haka kayi wa iyalin ka magana, ka gaya musu me ka saka a gaba, kuma zaka yi kokari wajen tabbatar wa basu wahala ba, ko ka bar su da yunwa. Ka gaya musu baro-baro irin kasada da hadari dake cikin wannan sabuwar sana’a da muhimmancin zuba lokacin ka da karfin ka domin cimma nasara. Ka shirya iyalanka ko ‘yan gidan ku yadda ya kamata sannan ka tambaye su suyi wannan tafiya da kai.

  1. KUDADEN DA KAKE SAMU BAZA MA SU BIYA UWAR JARIN DA AKA SAKA BA

Shi fa dan kasuwa musamman mai fara sana’a shine mutumin da yake buga-buga da daukar babbar kasada wanda ba kowa ne zai iya ba.

Idan ka zuba uwar jari a cikin sana’a, kuma baka ga riba ta fara fitowa nan take ba, kawai ka cigaba da gashi. Idan har ka mika wuya kafin ka fara samun riba, to baza ka taba samun riba ba. Idan kuma har ya yanke shawarar dena sana’ar kafin ka fara samun riba, to ka tuna cewa a baya ka samu jari, saboda haka zaka iya sake samowa.

  1. KOMAI BAYA TAFIYA YADDA YA KAMATA

Ko karamin yaro baya kawai mikewa ya fara tafiya lokaci daya. To idan ya tashi, sannan ya fadi me ya kamata yayi? Ya zauna yayi ta kuka? A a, ya kara mikewa sannan ya sake gwadawa.

Mikewa tsaye na daga cikin wannan harka. Idan matsaloli suka addabi sana’a, wannan kawai ya nuna cewa ka sake mikewa ne ka kara gwadawa. A matsayin ka na dan kasuwa, na tabbata zaka iya samun nasara, saboda haka kar rugujewar sana’a ta firgita ka. Zaka iya sake mikewa ka gwada.

Yanzu da ka gama karanta wannan rubutun, je kayi abu daya ya yafi maka amfani a wannan rubutun.

Dr. Bello Galadanchi kwararre ne a koyar da kasuwanci da harshen Chinese. Yayi Karatun Firamari a Al-Iman School Jos, da Sakandari a Ulul Albab Science Secondary School Katsina, da kuma digrin farko a Jami’ar Pennsylvania dake Amurka. Yayi karatun MBA da PhD a China, sannan ya kirkiri Kasuwar Bello. Galadanchi yayi aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka, kuma yanzu haka yana binciken kimiyyar ilimi a kasar Sin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button