Abubuwan Da Zaka Kiyaye Yayin Rijistar N-Power Da Link Din Da Zakabi Kayi Rijista.
1- Idan ka kasance kana cikin sahun waɗanda suke shirin N-Power na baya(Batch A and B), ko ka ƙara cikewa ba zaka yi nasarar kasancewa a sahun sababbin da za’a ɗauka ba.
2- Idan nambar BVN ɗinka bai yi daidai da sunan da kayi rigistar N-Power ba zaka samu damar shiga sahun sababbin waɗanda zasu ci gajiyar sabon shirin ba
3- Idan kayi kuskure wajan saka nambar asusunka(account number) ko BVN. za’a hanaka shiga sabon shirin N-Power
4- Sannan idan baka yi nasara a gwajin da za’a gudanar a yanar gizo-gizo (online test) ba, duk da kasance gwajin zai kasance mai sauƙi. A nan ma ba zaka samu nasarar shiga sabon shirin N-Power ba
5- Idan kayi kuskure a wajan zaɓar matakin karatunka ko ajin da kake , ba zaka yi nasarar shiga sabon shirin N-Power ba. misali mai NCE dole ya cike NCE
Ga Link Din Da Zakabi Kayi Rijistar N-Power.
Npower.fmhds.gov.ng
Daga Mutawakkil Gambo Doko