Rahotanni

Adadin Mutanen Da aka Kashe Tsakanin Sokoto, Zamfara Da Katsina Acikin Makwanni Biyu Da Suka Gabata, Sun Kai 800+.

Inji Shaikh Yusuf Muh’d Sambo Rigachikun.

Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano

Fittacen malamin Addinin musulunci dake garin Kaduna matemakin shugaban Majalisar Malamai na ‘kasa na Kungiyar Izalah Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya bayyana Takaicinsa kan yadda Ake kashe Al’umma A garuruwan katsina sokoto Zamfara inda yace alissafin da yayi A kasa da makonni 2 kadai Ankashema sama da mutane 850

Sheikh Rigachikun yace baya ganin lefin shugaban kasa A tabarbarewar tsaro A yankin arewa yace shugaban kasa ya bawa arewa dukkan wani mu’kami A bangaren tsaro sune kadai Suka ‘kiyin Abunda ya Dave

Sheikh Rigachikun yakara da cewa kisan ran Dan Adam babbban lefine awajen ubangiji yace yafi sauki mutum ya rushe dakin ka’aba Akan ya kashe ran mumini daya yace manzon Allah S A W yace ” duk Wanda ya temaka Aka kashe Ran mumini daya Koh da da Rabin kalma ne toh la’antar Allah da fushin Allah da Azaba sun tabbata akanshi”
Shehin malamin Yana wanan tsokacin ne A yayin da yake Gabatar da hudubar juma’a A massalacin Tunawa da Sheikh Abubakar Gumi dake Garin Rigachikun Ajahar Kaduna.

A ‘karshe malamin yayi Addu’ar Allah yakawowa nijeriya dauki daga miyagun ‘yan ta’addah

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button