Adams Oshomole Ya Tsallake Rijiya da baya, ‘Yan Sanda 2 Sun Mutu a Edo.
Jaridar SaharaReporters ta tarawaito cewa wata babbar mota ta kutsa kai tsakiyar jerin gwanon motocin yayin da tsohon gwamnan na jihar Edo, kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshomole zai tafi taron siyasa a Usen, karamar hukumar Ovia dake kudu maso gabashin Jihar Edo.
Wata majiya da ke kusa da Oshiomhole ta ce ya tsere cike da fargaba.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Osagie Ize-Iyamu, ya bayyana hatsarin a matsayin makircin kashe tsohon gwamnan jihar ne wato Oshomole Inji Shi.
Iyamu a wata sanarwa ya kuma dakatar da dukkan ayyukan yakin neman zaben sa.
Ya ce, “Ina son in mika ta’aziyyata ga iyalai, abokai, da duk wadanda suka san‘ yan sanda biyu na kwarai da muka rasa a yau a cikin mummunan hatsarin da ya afku da ayarin Adams Oshiomhole tare da sauran shugabanni zuwa taron yakin neman zabe a garin Usen a karamar hukumar Ovia dake Kudu maso gabashin Jihar.
“Tun daga lokacin mun dakatar da duk wasu shirye-shiryen yakin neman zabe da aka tsara a yau kuma muka shiga kokarin tare da, Adams Oshiomhole don tabbatar da kyakkyawar kulawa ga wadanda suka jikkata
“Yanayin hatsarin yana da ban mamaki da tada hankali, yadda babbar motar ta shigo cikin tawagar yan siyasar inji ganau.
“Yayinda muke jiran kammala binciken‘ yan sanda dangane da rokon da muka gabatar, ina kira ga mabiyan jam’iyyarmu a fadin jihar da su kwantar da hankulansu kuma su yi Addu’ar Allah Ya yi wa mamatan rahama Inji Shi.
Ahmed T. Adam Bagas