A Ajiye Batun Wajabta Sanyi Hijabi A Gefe A Fuskanci Matsalar Tsaro, Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN Ta Fadawa Majalisa”

Dan majaliaar tarayya, Musa Sa’idu Abdullahi dake wakilatar mazabun Bida/Gboka/Katcha daga jihar Naija, wanda shine ya dauki nauyin kudirin dokar halattawa mata saka hijabi a duka wani gurin taron jama’a a kasarnan, ya zauna da kungiyar Kiristoci ta CAN ya musu bayanin yanda Kudirin nasa yake.

Kudirin a yanzu ya wuce matakin karatu na 2 a majalisar wakilai. Saidai CAN ta bayyana cewa a dakatar da wanna kudiri.

Kungiyar ta CAN Tace ai akwai dokar data baiwa kowa kariya kada a nuna masa kyama bisa addinin da yake.

CAN tace ya kamata a mayar da hankali ne kan matsalar tsaro data addabi kasarnan, ta koka da cewa tana tafka asara sosai musamman a bagaren zuwa guraren ibadarta masu tsarki, saboda matsalar tsaron.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *