Abinda yasa ake hasashen a bana ma watan Ramadan zai yi kwana 30, “Cewar Sheikh Muhammad Hadi Balarabe”

Na fara wannan rubutu na ƙididdigar tafiyar watan Ramadan 1442hjr da ƙarfe sha biyu da minta arba’inda biyar (12:45) na rana – a ranar Lahadi 25/04/2021- idan ƙididdigar ta yi daidai, to akwai yiwuwar bana muyi azumi 30.

Saboda a yau mun ɗauki azumi na 13, kuma idan aka lissafo tun daga lokacin tsayuwar Watan, a (ranar Litinin 12/04/2021), zuwa yau daidai lokacin da na fara rubutun Watan ya cika awoyi ɗari uku da goma shatara (319) da minti goma shabiyu (12); ma’ana, kwana 13 da awa tara 7 da minti 12, kenan a cikin kwanan shi na goma shahuɗu (14) har ya riga ya cinye awa bakwai (7) da minti goma shabiyu (12), amma gashi lissafin azumin muna kan na goma shauku (13).

A lokacin da rana ta faɗi – ranar Lahadi 25/04/2021 – (da magariba) Watan za ya kasance yana da awa 326 da minti 25 watau kwana 13 da awa 14 da minti 25. Amma kuma yayin da Alfijir zai keto gobe Litinin da ƙarfe 4:57 (biyar saura minti uku) Watan zai kasance ya cika awa 338 da minti 24 watau kenan (a lissafin awoyi) ya kwana 14 da awa 2 da minti 24. Wannan na nufin tunda asubar ranar yau Litinin 26/04/2021, bisa ga lissafin awoyi, Watan ya cika kwanaki 14 cif-cif har ya yi awa 2 da minti 24; watau a cikin kwanan shi na 15!

Duba ga cewa kafin ɓullar Watan Ramadan, sai da Watan Sha’aban ya faku da fiye da awa14 kana jinjirin Watan Ramadan ya tsaya, ranar Litinin 11/04/2021 muka tashi da Azumi ranar Talata 12/04/2021. Idan lissafin ya ɗore a haka, insha’Allahu, ana hasashen cewa shima Watan Ramadan zaya tsaya ne a ranar Talata 11/05/2021.

Idan aka lussafa daga Talatar da muka ɗauki azumi 12/04/2021 zuwa Litinin 10/05/2021 za a samu kwana 29 (anyi azumi 29) kenan. Amma har rana ta faɗi watan bai kai matsayin da zaya baiyana a “Jinjirin Wata”ba. saboda haka za a tashi da azumi na 30 a ranar Talata; a wayi gari Laraba ayi Idil-Fitir, Insha’Allah.
Duka wannan hasashe ne.

Sai dai ƙarshen magana muce Allahu A’alam!

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *