Azumi:Buhari ya bukaci yan Najeriya da su tallafawa marasa karfi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci dukkanin yan kasa da su nuna kauna ga miliyoyin masu karamin karfi tare da tuna wadanda rikici ya raba da muhallansu a sadaka da addu’o’i a wannan muhimmin lokaci.

A cewar wata sanarwa daga babban mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kai, Malam Garba Shehu, Buhari ya bukaci Musulmin Nijeriya da su yi hakuri da juriya da kin amincewa da duk wata manufa da ke neman raba kan al’umma.

Buhari, a cikin sakon da ya aikawa kasar don bikin, ya roki Allah da ya karbi ibadun jama’a da aka yi a wannan lokacin sannan ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya kara hadin kai, zaman lafiya da ci gaban kasar.

Shugaban kasar yanzu haka yana Landan, Ingila (UK) domin hutun ganin likita kuma ana sa ran zai dawo Najeriya a wannan watan.

Ya kuma yi maraba da wannan watan Ramadan mai alfarma wanda ya kama farawar kwanaki talatin na azumi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *