Ban Yarda Ku Zagi Kowa Ba, Ko Ku Yiwa Wani Raddi Don Ya Aibanta Niba, Gargadin Ministan Sadarwa Sheikh Pantami, Ga Magoya Bayansa.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital, Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bukaci masoyansa da ka da su tayar da hankali game da kage da sharri da wasu suka yi masa.

Ministan yace, ka da wani daga cikin magoya bayansa su zagi wani ko su daki wani a madadinsa don ya zageshi ko ya mishi sharri.

Ministan ya bayyana hakan ne a wajan tafsirinshi na jiya Asabar, inda yake cewa;

“Duk wanda yake tare dani ban yarda ya zagi wani ba, ban yarda ya yi wa wani kazafi ba, ban yarda ya aibata wani ba, ban yarda ya daki wani ba, ban yarda ya yi komai ba.

“Idan mutum ya yi maganar da ka ga bai dace ba; ka yi masa nasiha. Idan ya zo da labarin da bai dace ba ko gaba da gaba ne ko a rubuce ne kace masa ba haka bane ka gyara. Idan ya dauka fani’ima idan bai dauka bar shi da Allah.

Daga Comr Abba Sani Pantami

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *