
Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya bayan nan ne dai majalisar dokokin jihar Kano ta bada umarnin a tsaya da duk wani gini da akeyi a masallatai da suke Kano.

Biyo bayan wannan umarni da majalisar ta bayyana, yanzu haka an fara rushe gine ginen da akayi a jikin masallacin juma’a dake Fagge.

Tun a wancan lokacin manyan malamai
Irin su Sheikh Tijjani Bala Ƙalarawi da ilahirin zauren malamai na Jihar Kano sai da suka fito suka yi tofin Allah tsine da waɗannan gine gine.


Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru