Duk Da Rashin Samun Tabbacin Ganin Wata Wani Malami Ya Gudanar Da Sallar Idi A Sokoto.

Duk da Bayanin da aka bayar na rashin samun tabbacin ganin Sabon jinjirin watan Shawal a Najeriya Daga Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alh Sa’ad Abubakar III, Wani Malamin Addinin Musulunci a jihar Sokoto Sheikh Musa Ayuba Lukuwa, ya gudanar da Sallar Idi tare da Mabiyan sa a Masallacin sa dake Unguwar Mabera a yau laraba.

Tun a Daren jiya Malamin ya sanar da Mabiyan sa cewa sun Sami tabbacin ganin wata a wasu wurare, Wanda shine ya Basu damar aje Azumi tare da gudanar da Sallar idi ayau.

Sai dai wasu na kallon Malamin a matsayin Wanda ya jima baya bin Umurnin Majalisar Sarkin Musulmi.

Mutane da dama ne suka Halarci Sallar idin Mai raka’oi biyu da aka Gudanar a Masallacin da dake Unguwar da ta Mabera.

Wakilin Mikiya dake Sokoto ya Garzaya unguwar tare da Jin ra’ayoyin wasu da suka sallaci sallar ta yau,

Wani Mai suna Ibrahim Bello da yayi tattaki Daga unguwar su zuwa Masallacin yace “shifa Yana da hujjoji na aje azumin sa a yau
Saboda ya fahimci cewa ana amfani be kawai da ilmin Falaki a Sha’anin ganin wata a najeriya”

Yanzu dai hankulla sun karkata a jihar Sokoto tsakanin wadanda suka bi Umurnin Sarkin Musulmi wajen cigaba da yin Azumi ayau,

Yayin da wasu ke ganin tunda sun Sami tabbacin Daga wasu wurare na samun ganin watan Shawal ba abinda zai Sanya su aje azumi ayau tare da gudanar da bukukuwan Sallah.

Daga Murtala ST Sokoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *