Duk Iskanci da kafircin da zakiyi ba za kikai Fir’auna da Abu Jahil ba, Martanin Kabiru Ado Muhd ga Muneerat Abdussalam.

Fir’auna wani kasurgumin kafiri ne da akayi a zamanin Annabi Musa (A.s). Annabin Allah Musa ya nunawa Fir’auna mu’ujizozinsa kala-kala, kuma Fir’auna ya tabbatar da cewa babu wanda ya isa yayi haka sai Annabin Allah.

Hasali ma har bokayen Duniya Fir’auna ya tara domin su kure Annabin Allah Musa amma suka kasa, amma duk da haka Fir’auna bai bada da Gaskiya Annabi Musa(A.s) ba. Kai daga karshe ma cewa yayi shine Allah, kuma duk lokacin da Fir’auna yake so yayi wani abu wanda yasan lamari ne na Ubangiji sai ya roƙi Allah ya taimakeshi. Daga karshe Fir’auna ya yi Mutuwa ta wulakanci ta kaskanci.

Abu Jahil wani tantirin kafiri ne wanda ya shahara wajen nuna tsagwaron kiyayya ga Annabi Muhammad (s.a.w) da addinin Musulunci.

Babu shakka Abu Jahil ya kasance makiyin addinin Musulunci da musulmai, kuma ya cutar da Annabi (s.a.w) da sahabbansa, amma daga Karshe shima ya yi Mutuwa ta kaskanci da wulakaci.

Babban abin da yakamata mutane su lura dashi acikin rayuwar Abu Jahil da Fir’auna shine, har yau baka taba jin wani kafiri ya sakawa Dansa suna Fir’auna ko Abu Jahil ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.