Addini

Hukumar Hisba ta cafke Karuwai 44 tare da wasu mutane 17 a Jihar Jigawa.

Spread the love

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Hukumar Hisba a Jihar Jigawa ta cafke karuwai aƙalla 44 tare da wasu lalatattun mutane 17.

Malam Aminu Dahiru, babban Kwamanda a hukumar ta Hisba ne ya bayyana hakan ga manema labaru, yau Talata a garin Dutse.

Ya bayyana cewa mutanen, an kama su ne a ƙauyen Gujungu yayin da hukumar Hisba take sintirin aiki tare da taimakon jami’an ƴan sanda.

An kuma miƙa waɗanda aka cafke ɗin zuwa babbar Kotun Majistiri da take ƙaramar hukumar Ringim.

A ƙarshe, Mista Dahiru, yayi kira ga al’umma musamman matasa, akan su gujewa duk wani aikin lalata da zai iya rusa rayuwarsu a nan gaba, tare da haddasa matsaloli a cikin al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button