Karku bari Malamai su rinƙa amfani da ku wajen biyan buƙatunsu ko su zuga ku domin ku zaɓi wani Ɗan siyasa. ~Cewar Sheikh Maqari

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Shehin Malamin ya bayyana cewa talakawa su daina bari kwaɗayayyun Malamai suna amfani dasu wajen neman kuɗi, kuma suna umaratarsu su zaɓi ƴan Siyasa.

Maƙari ya bayyana haka ne cikin wani gajeran faifan bidiyo nasa da yake yawo a kafafen sada zumunta.

Ferfesan ya ƙara da cewa, Duk Malamin da ya kawo muku tallar wani ɗan siyasa, to ku ce masa ya rantse da Al-Qur’ani akan ba kuɗi aka bashi ba, kafin ku yarda da shi.

One thought on “Karku bari Malamai su rinƙa amfani da ku wajen biyan buƙatunsu ko su zuga ku domin ku zaɓi wani Ɗan siyasa. ~Cewar Sheikh Maqari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *