Addini

Majalisar Wakilai Zata Yunkuro Kan Makarantun Allo.

Spread the love

Majalisar tarayya zata fara tattauna yadda makarantun Allo zasu samu kulawa irin na makarantun Boko a Kasar Nan.

Majalisar wakilan Najeriya ta karbi wani kuduri mai neman a amince da wani tsari da zai ba makarantun allo matsayi da Inganci a kasar Nan, tamkar yadda ake ba makarantun boko.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Bodinga, Dange Shuni da Tureta Dr. Balarabe Shehu Kakale ya ce baiwa daliban makarantun allo matsayi zai kara ba su kwarin gwiwa su bayar da tasu gudunmuwa wajen samar da ci gaban kasa.

A cewarsa mafi yawa daga cikin wadannan daliban suna da basira da hukumomin za su yi amfani da su wajen gina kasa.

A arewacin Najeriya, jahar Sokoto na Daga cikin jahohin da suka samar da wani tsari na kyautata sha’anin almajirai.

Dr. Umar Altine Dadin Mahe, sakataren zartaswa na hukumar larabci da addinin musulunci shi ne jagoran shirin na gwamnatin jahar ya ce wannan tsari idan aka amince da shi a matakin kasa zai taimakawa jihohi kamar jihar Sokoto wadda dama ta kudurci sake fasalin tsarin almajirci ta yadda dalibai za su daina bara.

Bisa ga la’akari da kasancewar Najeriya kasa daya mai kabilu da addinnai mabambanta ko yaya masana ke kallon yiwuwar aiwatar da irin wannan tsarin a kasar?

Farfesa Tukur Muhammad Baba na sashen nazarin halayyar Dan Adam a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Birnin Kebbi ya ce tsarin yana da kyau amma sai an cire batun siyasa ko addini sannan a yi masa kwakkwaran tsari ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.

Shin Masu Karatu ya Kuke kallon Wannan Al’amari ???

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button