Ramadan; An ragewa ma’akata Musulmi loƙacin aiki a Jami’ar “University Of Jos”

Hukumar gudanarwa a Jami’ar Jos (University of Jos) ta rage loƙacin aiki ga ma’aikata-Musulmi yayinda suke gudanar da ibada a watan Azumi.

Mataimakin Rijistara Abdullahi Abdullahi ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labaru yau Alhamis a garin Jos dake Jihar Plateau.

Ya kuma ƙara da cewa an tabbatar da wannan kuɗiri ne domin baiwa ma’aikata-Musulmi a Jami’ar damar gudanar da ibada cikin sauƙi, musamman a irin wannan loƙaci na Azumi.

Har’ilayau; Mataimakin Shugaban Makarantar (Vice Chancellor) Farfesa Sebastian Maimako shine ya sanya hannu da kuma amincewa da kuɗirin.

A ƙarshe; Mr Abdullahi ya bayyana yadda Mataimakin Shugaban Makarantar yayi kira ga ɗaukacin al’ummar Musulmi musamman malamai, ɗalibai da dukkanin ma’aikata a Jami’ar da suyi amfani da wannan loƙacin na Ibada wajen addu’o’i domin samun cigaba, yalwatar arziki da zaman lafiya a makarantar, jihar Filato dama ƙasa baki ɗaya.

Daga Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *