Ramadan: Bambanci tsakanin azumin Musulmi da na Kirista

Masallaci da coci

Azumin watan Ramadan yana daya daga cikin ginshikan Musulunci guda biyar da suka wajaba a kan kowane Musulmin da ya kai munzalin yi – baligi, mai hankali, kuma mai cikakkiyar lafiya.

Kamar yadda yake a Musulunci, mabiyan wasu addinai ma kamar addinin Kirista suna gudanar da azumi.

Sai dai akwai bambance-bambance tsakanin azumin mabiya addinin Musulunci da kuma na Kirista – ko da yake dukkansu suna yin azumin domin neman kusanci ga Ubangiji.

Malamai da dama sun bayyana cewa bambance-banbancen sun hada da cewa Musulmai na yin azumi na kwanaki 29 ko kuma talatin kamar yadda hadisi ya tabbatar daga Manzon Allah (SAW) cewa, wata a Musulunci yana yin kwana 30 ne ko kuma 29, don haka azumi zai iya kasancewa kwana 30 ko 29.

Amma kuma bayanai sun nuna cewa a addinin Kirista ba haka ba ne wanda su azuminsu na kwana 40 ne domin sun yi imanin cewa annabi Isa (AS) ya zauna kwanaki 40 bai ci abinci ba wanda aka ruwaito cewa a wannan lokacin ya yi sadaka ya yi addu’oi yayin azumin.

Ustaz Murtala Muhammad Gusau, limamin Masallacin Jumma’a ne da ke garin Okenen jihar Kogi a Najeriya, kuma shugaban wata cibiyar yada addinin Musulunci da karantarwa a garin na Okene, kuma a tattanawarsu da BBC ya ce akwai banbance-banbance sosai tsakanin azumin Muslmai da na Kirista har ma da na Yahudanci.

”Azumi dai shi ne bautawa Allah ta hanyar kamewa daga cin abinci da abin sha da jima’i, tun daga hudowar alfijir har zuwa faduwar rana”.

A kowace shekara cikin watan Ramadan Musulmai a fadin duniya na gudanar da azumin kwanaki 29 ko 30, wanda ya sha banban da na mabiya addinin Kirista da na Yuhudanci da su kan yi azumin kwana 40 ne.

Ya kara da cewa ”Amma duka manufarsu kusan daya ne – Musulmai na yin azumi a bisa bin umarnin Allah da nufin gyara dabi’u da halayyar al’umma ta zama mai tsoron Allah, sannan kuma a tunatar da Musumai game da watan da aka saukar da Alkur’ani mai girma wato cikin watan Ramadan.”

Sheik Ibrahim Adamu Disina wani fitattaccen malami ne a jihar Bauchi arewa maso gabashin Najeriya, ya yi wa BBC karin bayanin cewa Musulmai kan fara azumi tun daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana inda su kan kauracewa ci da sha da jima’ai.

”Musulmai na azumtar kwanaki 29 ko 30, yayin da Kiristoci ke azumtar darare 40 da yini 40 ko kuma kwana 40, amma ko wanne akwai banbance-banbance ajen yanayin da bangarorin biyu ke azumin”.

”Kiristoci kan yi azumin ne ba tare da ya hana musu cin wasu abubuwa ba,” in ji shi.

Haka shi ma Ustaz Murtala ya yi karin bayani cewa , Kiristoci na yin azumin a duk shekara amma kuma kamar yadda Musulunci ya tanadi cewa ya zama wajibi a kan duk Musulmi baligi, mai cikakkiyar lafiya ya dauki azumin watan Ramadan ba, su Kiristoci ba kowa ne ya ke yi ba kua bai zama wajibi ba.

”Yawanci malamansu da sauran jagororinsu ne kawai suke yin azumin, sannna kuma suna iya zamantowa mutum gashi yana azum amma zai iya cin wasu abubuwa abin sha ne kawai ba za i sah ba, ko kuma ya kasance ba zai ci ba gaba daya har tsawon kwana 40,” in ji malamin.

Daga; Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *