Taƙaitaccen tarihin Sheikh Sudais

TAƘAITACCEN TARIHIN BABBAN LIMAMIN HARAMIN MAKKAH🕋 SHEIKH ABDUR RAHMAN AS-SUDAIS

Cikakken sunansa shi ne Abdur-Rahman Ibn Abdul’Aziz Bin Muhammad Bin Abdullahi wanda ake yi masa laƙabi da As-Sudais .Abdur Rahman As-Sudais shi ne shugaban limaman Haramin Makkah, kuma shugaban hukumar kula da haramin Makkah da Madinah. An haifeshi a ranar 10 ga watan Febrairu 1960 (1382 hijiriya)a birnin Riyadh na ƙasar Saudiya. Ya fito daga cikin wata ƙabila mai suna Anzah.

Sheikh As-Sudais ya haddace Al-Ƙur’ani tun yana ɗan shekaru 12 kacal a duniya.

••••••••ILMI

Sheikh Sudais yayi kararun elementary a makarantar Al-Muthanna Bin Harith dake birnin Riyadh. Ya kuma kammala karatun sikandare a shekarar 1979. Daga yayi nan yayi karatun digirinsa na farko a tsangayar shari’a a jami’ar birnin Ridadh, ya kuma kammala a shekarar 1983. Yayi digirinsa na biyu wato (masters) a cikin shekarar 1995. Sannan yayi digirin digirgir (Doctorate) duk a fannin shari’a .

Sannan yayi karatun Al-Ƙur’ani mai girma a birnin Riyadh ,inda yayi karatu a wajen malamai kamarsu Muhammad Abdul-Majid Zakir , Abdur-Rahman Bin Abdul-Aziz Al- Rayyan da Sheikh Muhammad Ali Al-Hassan.

•••••••LIMANCI 🕋

A Shekarar 1982 (1404 Hijiriya) aka naɗa Sheikh Abdur-Rahman As-Sudeis a matsayin limamin babban masallacin Harami dake birnin Makkah a loƙacin yana da shekaru 24 a duniya. Farkon sallar da Sheikh Sudais ya jagorarta a haramin Makkah ita ce sallar La’asar a ranar Lahadi 22 ga watan Sha’aban na shekarar 1404 . Farkon sallar juma’ar daya jagoranta ita ce a ranar 15 ga watan Ramadana a shekarar 1404 (24 July 1984)

A ranar 17 ga watan Jumada Akhir na shekarar 1433 (2012) , Marigayi Sarki Abdullahi Bin Abdul-Aziz Al-Saud ya bada umarnin naɗa Sheikh Farfesa Abdur-Rahman As-Sudeis a muƙamin shugaban hukumar kula da haramin Makkah da Madinah, daidai da muƙamin minista.

Shiekh Sudeis yana da ƙoƙari sosai wajen ziyarar ƙasashen musulmai domin gabatar da lactoci ko buɗe masallatai. Haka nan yana da gabatar da darussa a masallacin haramin Makkah.

••••••MUƘAMAI

Baya da limanci a masallacin Ka’aba , Sheikh Sudeis ya riƙe ya muƙamai irinsu:

√Lecturer a tsangayar shari’a a jami’ar Ummul-Qura dake Makkah

√Mataimakin Farfesa a tsangayar shari’a jami’ar Ummul-Qura dake Makkah

√ Farfesa na Usoolul-Fiqh a jami’ar Ummul-Qura dake Makkah.

•••••••LAMBAR YABO

Sheikh Sudais shine ya lashe kyautar karatun Al-Ƙur’ani mai girma na duniya da aka gudanar a Dubai a shekarar 2005.

Happy Juma’at 🕌

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *